Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a ranar 13 ga Oktoba. Shugaban ƙasa na kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya ce matakin ya biyo bayan taron majalisar koli ta ƙasa (NEC) da aka yi har zuwa ƙarfe 4:00 na safe.
ASUU ta ce ta yanke wannan shawarar ne bayan gwamnatin tarayya ta dawo teburin tattaunawa kan sabunta yarjejeniyar 2009, duk da cewa akwai sauran abubuwa da za a gyara kafin a cimma matsaya. Kungiyar ta bayyana cewa matakin na nufin nuna godiya ga dalibai, iyaye, da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) bisa ƙoƙarinsu wajen kawo sulhu.
ASUU ta jaddada bukatunta da suka haɗa da kammala yarjejeniyar 2009, sakin albashin watanni uku da rabi da aka rike, inganta tallafin jami’o’i, da daina tsangwamar malaman jami’o’in LASU, FUTO, da Prince Abubakar Audu University.
