Yusuf Buhari, ɗa namiji tilo na marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai a zaɓen 2027. Ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da ya sanya wa hannu mai ɗauke da ranar 3 ga Afrilu, 2026.

A cikin wasiƙar, Yusuf ya ce yana da burin tsayawa takarar kujerar mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, ya yanke shawarar shiga takarar domin bayar da gudunmawa wajen samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba ga al’ummar yankin.

Rahotanni sun nuna cewa matakin nasa ya zo ne bayan shugabannin APC a ƙaramar hukumar Sandamu sun bayyana goyon bayansu gare shi a wani taro da suka gudanar. An kuma ce gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, na daga cikin waɗanda ke mara masa baya a wannan takara.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version