Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen cewa hauhawar farashi a Najeriya zai sauka ƙasa da kashi 10 cikin ɗari kafin ƙarshen shekarar 2026. Wannan bayani ya fito ne ta bakin mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar Juma’a, 9 ga Janairu, 2026.
Onanuga ya bayyana hakan ne bayan yabon dq shugaban ƙasa ya yi wa kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX) bayan darajarta ta kai sama da naira tiriliyan 100. Ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnati ke aiwatarwa za su sa shekarar 2026 ta kasance mafi alheri ga masu zuba jari, tare da ƙara bunƙasar tattalin arziki.
A cewar Onanuga, an samu raguwar hauhawar farashi daga kololuwar kashi 34.8 a Disambar 2024 zuwa kashi 14.45 a Nuwambar 2025, sakamakon tsauraran matakan kuɗi da saka jari a aikin noma. Ya ƙara da cewa ana sa ran hauhawar farashin zai kai kashi 12 a 2026, tare da yiwuwar saukowa ƙasa da kashi 10, lamarin da gwamnati ke ganin zai inganta rayuwar ’yan ƙasa da haɓaka tattalin arziki.
