A daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke shirin gudanar da zaɓen fidda gwani, ‘yan majalisar wakilai 28 sun sauya jam’iyya a rana guda domin neman damar samun tikiti. Sauyin ya shafi manyan jam’iyyu ciki har da APC, PDP, LP, NNPP da wasu ƙananan jam’iyyu.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙa akwai Philip Agbese daga APC zuwa LP, yayin da Akanni Clement Ademola ya koma Accord Party daga PDP. Haka kuma Ugochinyere Ikeagwuonu da Nwogu Mathew sun koma APP, yayin da wasu ‘yan LP da dama suka koma ADC.

Jam’iyyar APC ta karɓi ‘yan majalisa da dama musamman daga Arewa, ciki har da wasu daga Kano da suka bar NNPP zuwa APC. ‘Yan majalisar sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyunsu ne suka sa suka ɗauki matakin sauya sheƙa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version