Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sanya harajin shigo da fetur da dizal na kashi 15 cikin 100, matakin da ta ce zai taimaka wajen ƙarfafa masana’antar tace mai a cikin gida da rage dogaro da kasashen waje. Kakakin shugaban kasa kan yada labarai, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, yana mai cewa wannan mataki “ ci gaba ne, ba nauyi ba,” domin gina karfin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samun ‘yancin makamashi.
Dare ya ce, duk da cewa Najeriya tana cikin manyan masu fitar da danyen mai a duniya, shekaru da dama tana kashe daloli wajen shigo da mai da aka tace daga kasashen waje, abin da ke jawo asarar kudaden musayar kasashen waje da kuma rasa ayyukan yi a gida. Ya ce sabon harajin zai sa shigo da mai daga waje ya yi tsada, hakan kuma zai bai wa matatun cikin gida irin su Dangote da Port Harcourt damar yin gogayya cikin sauki.
Fadar shugaban kasa ta kara da cewa, yayin da matatun cikin gida suka fara tace mai da yawa, farashin fetur zai fara daidaituwa, sannan za a samu karin ayyukan yi da jari daga kamfanoni masu zaman kansu. Dare ya ce, wannan matakin ba nauyi bane, illa wata hanya ce da gwamnati ke bi don kai kasar daga dogaro zuwa cin gashin kanta a bangaren makamashi.
Sai dai, ‘yan kasuwar mai sun nuna damuwa cewa farashin fetur na iya wuce N1,000 a kowace lita sakamakon wannan sabon haraji. Amma gwamnati ta ce, duk da wannan karin farashi na dan lokaci, matakin zai tabbatar da dorewar kasuwar makamashi da jawo hannun jari na dogon lokaci. Harajin zai fara aiki ne bayan kwanaki 30 — wato daga ranar 21 ga Nuwamba, 2025.
