’Yan sanda a jihar Legas sun sake cafke wani tsohon fursuna mai suna Segun Kolawole, dan shekara 25, kwana biyar kacal bayan an sake shi daga kurkukun Kirikiri Correctional Centre. An kama shi ne bisa zargin komawa ga aikata laifin fashi da yankan aljihu, tare da wasu abokan aikinsa biyu — Sodiq Isa (27) da Adekanmbi Ganiu (21).

Labarin ya nuna cewa jami’an ’yan sanda sun damke Kolawole ne da safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan sun lura da motsinsa da ya haifar da zargi. Bayan bincike, an gano tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka tabbatar da cewa duk daga wani fashi da aka yi a Opebi ne, inda aka sace ₦200,000 da waya daga hannun wani ɗan kasuwa.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta bayyana cewa Kolawole ya riga ya sayi kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sace, kuma duk an kwato su daga hannunsa. Adebisi ta kara da cewa jami’an RRS sun kuma cafke sauran abokan aikinsa biyu a wani samame daban da aka gudanar a ranar Juma’a da yamma, inda ake zargin suna yunkurin satar wayoyi daga hannun fasinjoji a wurare daban-daban na Legas.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa za a gurfanar da mutanen gaba ɗaya a gaban kotu bayan kammala bincike, domin girbar abin da suka shuka. Wannan na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro ke ƙara kaimi wajen yakar laifukan fashi, sata da yankan aljihu a jihar Legas da kewaye.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version