Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta kwato sama da wuraren hakar ma’adinai 90 daga hannun masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, tare da tara sama da naira biliyan 28 a shekarar 2024. Ministan Ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayyana haka yayin taron tattaunawa tsakanin shugabannin yankin Kudu maso Yamma da kungiyar Afenifere a Legas. Ya ce ma’aikatarsa ta zarce abin da aka ware mata a kasafin kudin bana, inda ta kafa rundunar musamman tare da NSCDC domin kare wuraren hakar ma’adinai daga barayin kasa.

Alake ya bayyana cewa fiye da mutane 300 an kama su saboda hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, 50 daga cikinsu ana shari’a da su yayin da 20 suka riga da aka yanke musu hukunci. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ta hana fitar da ma’adinai a asalin su ba tare da an sarrafa su a cikin gida ba, domin kara darajar tattalin arzikin kasa da samar da ayyukan yi.

Ministan ya gargadi sarakunan gargajiya da kada su rika hada kai da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba saboda kudi, yana mai cewa “makomar kasar nan ba ta da farashi.” Ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin tabbatar da bin doka a harkar hakar ma’adinai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version