Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Yanar Gizo ta Jihar Kano ta bayyana matuƙar alhini da jimami kan rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu, Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji, waɗanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Ungogo da Birnin Kano. Ƙungiyar ta bayyana rasuwar a matsayin babbar rashi da ta girgiza Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
A cikin saƙon ta’aziyya, Shugaban Ƙungiyar, Kwamared Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo, ya ce mutuwar ‘yan majalisar biyu ta bai wa kano giɓi na hazikan wakilai masu kishin jama’a, waɗanda muradunsu, basirarsu da jajircewarsu suka taimaka wajen inganta wakilci da tafiyar da mulki. Ya bayyana rasuwar a matsayin gibi mai raɗaɗi a majalisar dokoki wanda zai yi matuƙar wahala a cike shi.
Ɗangambo ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayan, Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore, da sauran ‘yan majalisar da al’ummar Kano gaba ɗaya. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayan, Ya ba iyalansu da jihar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.
