Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Filato ta musanta rahotannin da ke cewa akwai wata ƙungiyar Musulmi da ke shirin kafa hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Sakataren JNI na jihar, Dr. Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar Musulmi da ta sanar da irin wannan shiri, yana mai cewa rahoton ya samo asali ne daga wasu hotuna da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI aka yaɗa a kafafen sada zumunta.
Ya bayyana cewa ba za a iya kafa hukumar Hisbah a hukumance ba sai da dokar Majalisar Dokokin Jihar Filato, yana mai cewa babu irin wannan doka da gwamnati ta kafa.
JNI ta kuma buƙaci gwamnati da masu amfani da shafukan sada zumunta su riƙa tantance bayanai kafin yaɗa su, domin kauce wa tayar da hankula da kuma kare zaman lafiya a jihar.
