Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya, EFCC, ta bukaci tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da ya miƙa kansa domin amsa tambayoyi kan zargin almundahana da ya shafi dala miliyan 14.86.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan yayin mayar da martani kan zargin da Sylva ya yi cewa hukumar ta fara gudanar da ayyukanta kamar wata hukuma ta jam’iyyar APC maimakon ta gwamnati.

Sylva, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, ya ce ya aika wa EFCC kwafin wasikar murabus dinsa tare da zargin hukumar da ƙara mayar da ayyukanta na siyasa, yayin da ya ce ficewarsa daga jam’iyyar na iya jawo masa ƙarin bincike.

EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema tun Nuwamban 2025 bisa zargin haɗa baki da karkatar da dala 14,859,257, yayin da ake ci gaba da shari’a kan wasu zarge-zargen da ake masa, ba tare da an same shi da laifi ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version