Wata ƙungiya mai suna Kwankwaso Support Group 2027 ta ba da shawarar tsayar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027. Shugaban ƙungiyar, Abba Gwale, ya bayyana hakan ne a Kano a ranar Juma’a.

Gwale ya ce a matsayinsu na amintattun magoya bayan Kwankwaso, sun ga dacewar kiran ‘yan Najeriya da su goyi bayan haɗin Obi–Kwankwaso domin ceto ƙasar daga matsalolin tsaro, yunwa da talauci. Ya ce haɗin gwiwar na da nufin haɗa ƙarfin goyon bayan Obi a Kudu da kuma na Kwankwaso a Arewa.

Ya ƙara da cewa wannan haɗaka na da burin ƙwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulki tare da kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya. A cewarsa, Kwankwaso yana da magoya baya a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, musamman a tsakanin talakawan da ke fama da matsin rayuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version