Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe jami’an tsaro uku tare da yin garkuwa da mutum 11, ciki har da wani malamin addinin Kirista, a wani hari da suka kai a jihar Kaduna. Lamarin ya ƙara tayar da hankula a yankin da ke fama da matsalar tsaro.
Ƴan bindigar sun kai harin ne da asubahin ranar Asabar a ƙaramar hukumar Kauru. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya janyo asarar rayuka da kuma sace mutane da dama, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
A wata sanarwa, shugaban cocin Katolika na yankin Kafanchan, Very Reverend Father Jacob Shanet, ya bayyana abin da ya faru a matsayin mummunan lamari ga cocin da al’ummar yankin. Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun bazama domin nemo mutanen da aka yi garkuwa da su.
