Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake lashe zaɓen 2027, yana mai cewa jam’iyyar APC ce ke da cikakken iko a siyasar Kano.
Yusuf ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga magoya baya a gidan gwamnati bayan dawowarsa daga Abuja, inda ya halarci tarukan jam’iyyar APC. Ya ce ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a fannoni kamar tattalin arziki, lafiya, ilimi da ababen more rayuwa sun isa su tabbatar da nasarar Tinubu a karo na biyu.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa APC ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya cin zaɓe a Kano da ma ƙasa baki ɗaya, yana mai bayyana jam’iyyun adawa kamar ADC da NNPP a matsayin marasa ƙarfi, tare da alƙawarin ci gaba da kawo ci gaba a fannoni daban-daban ga al’ummar jihar.
