Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Kabiru Nuhu mai shekaru 27, bisa zargin banka wa mahaifinsa mai shekaru 60 wuta a ƙaramar hukumar Kazaure.
Mai magana da yawun rundunar, Shi’isu Adam, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya zuba wani abu mai ƙonewa da ake kyautata zaton fetur ne a jikin mahaifin nasa kafin ya banka masa wuta. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe a ranar 1 ga Afrilu, 2026 a unguwar Magama da ke garin Kazaure.
An ce an garzaya da wanda abin ya shafa asibiti, sai dai ya rasu yayin da yake karɓar magani. ‘Yan sanda sun ce an kama wanda ake zargin da raunukan wuta a jikinsa, kuma yanzu haka yana tsare, inda za a miƙa shi sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
