Fitaccen ɗan jarida, Malam Aliyu Abubakar Getso, ya rasu a safiyar ranar Lahadi 05 ga Oktoba. Rahotanni daga majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa Nigerian Tracker cewa Malam Getso ya rasu ne da sanyin safiya, kuma za a gudanar da sallar jana’izarsa a gidansa da ke Janbulo, cikin birnin Kano.
Kafin rasuwarsa, Malam Getso ya shafe shekaru yana aiki a kafafen yada labarai daban-daban a Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa a fagen gyaran harshe da fassara.
Ya fara aikinsa a Gidan Rediyon Kano, kafin daga bisani ya ci gaba da aiki a Freedom Radio, Vision FM, sannan kuma Premier Radio, wanda shi ne gidan rediyo na ƙarshe da ya yi aiki kafin rasuwarsa.
Malam Aliyu Abubakar Getso ya bar tarihi mai ɗorewa a harkar yada labarai a jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
