‘Yan bindiga sun sace kansiloli biyu masu ci da kuma wani Liman a daren Laraba 01ga Oktoba, a garin Tsauni, birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Kansilolin da abin ya shafa su ne na mazabu biyu, Gidan Goga da Tsibiri a karamar hukumar Maradun, inda aka ce an kama su da misalin ƙarfe 8:05 na dare, jim kaɗan bayan sallar Magrib, a kusa da ofishin ‘yan sanda.
Shugaban karamar hukumar Maradun, Hon. Sanusi Gama Giwa, ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana cewa waɗanda aka sace ɗin ‘yan majalisarsa ne.
A cewarsa, mutanen suna zaune ne a wajen shan shayi lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki.
“Lamarin ya faru ne a gaban ofishin ‘yan sanda inda jami’ai kan kasance. ‘Yan bindigar ma sun kwace wayoyin ‘yan sandan ba tare da wata turjiya ba. Ba su cutar da kowa ba,” in ji Giwa.
Ya ƙara da cewa maharan sun fito ne da niyyar kama wani mutum daga kauyen Kaura. Amma da suka kasa samun wanda suke nema, sai suka yi awon gaba da mutum shida, kafin daga baya su saki uku, sannan su ci gaba da tafiya da kansilolin biyu da Liman ɗin.
Garin Tsauni, inda aka sace mutanen, na ɗaya daga cikin wuraren da aka taɓa karɓar bakin ‘yan gudun hijira da suka tsere daga hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan da ke kewaye — lamarin da ya sake tayar da hankula kan raunin tsaron yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa tuni jami’an tsaro su ka bi sahun su, kuma a halin yanzu su na yin dik mai yiwuwa wajen ceto su.
“Muna yin duk abin da ya kamata don ceto waɗanda aka sace tare da tabbatar da an hukunta maharan,” in ji DSP Abubakar, yana kira ga al’umma da su rika ba da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaki da masu aikata laifuka.
