Gwamnatin Jihar Neja ta gargadi mazauna yankin bakin kogin Neja da na Kaduna su bar yankunan saboda za a saki ruwa daga manyan dam-dam na Kainji, Shiroro, Zungeru da Jebba.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar (NSEMA) ta ce ana sakin dubban lita na ruwa a kowane dakika, lamarin da zai iya haifar da ambaliyar ruwa mai tsanani a garuruwa da dama.

Shugaban hukumar, Abdullahi Baba-Arah, ya ce rahoton Hukumar ya nuna akwai hatsarin malalar ruwa, yayin da hasashen NiMet ya nuna ƙarshen damina zai zo da guguwar iska mai karfi.

Ya kuma bayyana cewa an riga an samu asarar gidaje, gonaki, gadoji da hanyoyi a wasu kananan hukumomi ciki har da Lavun, Mokwa, Lapai, Shiroro, Bida, Suleja da Mashegu, inda a wasu wuraren ma aka samu asarar rayuka.

Baba-Arah ya bukaci jama’a su guji tsayuwa ƙarƙashin itatuwa lokacin ruwan sama, su kuma nisanci gine-ginen da ba su da ƙarfi.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa ana cigaba da tantance illolin ambaliyar tare da samar da wuraren fakewa ga mutanen da ke cikin haɗari.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version