Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a yankin Tsafe na Jihar Zamfara, inda suka kashe jami’an tsaro guda takwas, ciki har da ’yan sanda biyar da jami’an Community Protection Guards uku. Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis a kusa da kauyen Gidan-Giye, a kan hanyar Gusau–Funtua, yayin da rundunar tsaro ke sintiri domin kare matafiya daga hare-haren da ke yawan faruwa a yankin.

Wani mazaunin yankin, Ya’u Musa, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun boye a daji kafin su bude wuta kan motar sintirin, inda suka kashe dukkanin jami’an nan take. Ya ce waɗannan jami’an an turo su ne daga gidan gwamnati na Gusau domin gudanar da aikin musamman na tabbatar da tsaron hanya, amma cikin ƴan mintuna bayan barin garin Tsafe ne aka ji karar harbe-harbe daga inda aka kai musu kwanton bauna.

Bayan harin, ’yan bindigar sun tsere cikin daji ta kan babura, yayin da aka dauki gawarwakin jami’an zuwa Asibitin Kasa na Gusau (Federal Medical Centre). Harin ya kara tayar da hankalin al’umma da ke fama da matsalar tsaro a yankin Tsafe da kewaye.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana jimaminsa kan kisan, tare da yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, ya roki Allah ya gafarta musu, tare da yin addu’ar kawo karshen matsalar tsaro a Zamfara da arewacin Najeriya baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version