Kungiyar International Federation of Journalists (IFJ) ta bayyana cewa mutane 128 masu aikin jarida ne suka mutu a fadin duniya a shekarar 2025, inda mafi yawan su ke Gabas Ta Tsakiya. Sakatare Janar na IFJ, Anthony Bellanger, ya ce wannan ba kididdiga kawai ba ce, amma gargadi ne ga ‘yan jarida a duniya baki daya.

IFJ ta nuna damuwa musamman kan yankin Falasdinu, inda aka samu mutuwar ‘yan jarida 56 yayin rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza. Haka zalika, an samu rahotanni kan mutuwar ‘yan jarida a Yemen, Ukraine, Sudan, Peru da India. Bellanger ya yi Allah wadai da rashin hukunci ga masu kai hare-hare kan ‘yan jarida, yana mai cewa hakan na baiwa masu kisa damar ci gaba da aikata laifuka.

Kungiyar ta ce har yanzu mutane 533 na aikin jarida suna cikin gidan yari a fadin duniya, inda China ta fi kowacce kasa da yawan ‘yan jarida a kurkuku 143, ciki har da Hong Kong. IFJ ta kara da cewa yawan mutuwar ‘yan jarida da ta kididdige ya fi na Reporters Without Borders saboda hanyoyin kirga daban-daban, har da mutuwar mutane 9 sakamakon hadura.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version