Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci tsohon shugaban NNPP na jiha, Hashimu Dungurawa, da ya daina tsoma baki a dukkan harkokin jam’iyyar har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta tabbatar da Hon. Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin Shugaban NNPP na riƙo a Jihar Kano, tare da amincewa da dakatar da Dungurawa daga jagorancin jam’iyyar.

Daraktan yaɗa labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce kotun ta sanya ranar 19 ga Janairu domin sauraron ƙarar da Exco na Dawakin Tofa suka shigar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version