Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a kan takardar lamuni na naira miliyan 500, tare da sharaɗin kawo mutum biyu da za su tsaya masa. Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite, ne ya yanke wannan hukunci.
Alkalin ya umurci cewa mutanen da za su tsaya masa su kasance masu filaye a Maitama, Asokoro ko Gwarimpa da ke Abuja, tare da tabbatar da takardun kadarorinsu a gaban magatakarda. Haka kuma, kotun ta bukaci su shaida wa kotu halin arzikinsu.
Kotun ta kara da cewa kwamishinan da masu tsaya masa za su mika fasfo dinsu ga kotu, kuma ba za su fita daga ƙasa ba sai da izinin kotu, tare da mika hoton fasfo biyu. An dage shari’ar zuwa 20 ga Janairu, 2026, yayin da EFCC ke zargin sa da halasta kuɗaɗen haram na kusan dala miliyan 9.7.
