Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kira ga ‘yan ƙasa da su kwantar da hankulansu, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar. Wannan bayanin ya fito ne bayan ganawar da shugaban ya yi da Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, wanda ya bayyana abin da aka tattauna.
Ministan ya ce shugaban ƙasar na bibiyar barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi a kan Najeriya, tare da tattaunawa da ƙasashen duniya domin bayyana irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen shawo kan matsalolin tsaro. Ya ce Tinubu na nazarin lamarin cikin kwanciyar hankali domin tabbatar da martabar ƙasar.
A cewarsa, sauya manyan shugabannin tsaro da aka yi cikin ‘yan makonni baya na daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka domin ƙarfafa tsaro da inganta dabarun yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro a ƙasar. Ministan ya ce gwamnatin na ci gaba da duba wuraren da ake buƙatar gyara.
Ministan ya kuma yi watsi da maganganun da ke cewa Najeriya ba ta mutunta addinai, yana mai nuna cewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya bai wa kowane ɗan ƙasa damar yin addininsa ba tare da tsangwama ba. Ya ce shugaban ƙasa na bibiyar dukkan lamarin cikin tsanaki, tare da fatan cewa al’amura za su daidaita a lokaci mafi kusa.
