Gwamnatin Tarayya ta mika gidaje 100 masu dakuna biyu ga wasu zawarawa a Rigachikun, Jihar Kaduna, a ƙarƙashin shirin Family Homes Funds Limited (FHFL). Gidajen, na cikin shirin samar da gidaje masu ɗorewa ga marasa ƙarfi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka a matsayin muhimmin ginshiƙi na Renewed Hope Agenda.
Shugaban FHFL, Demola Adebise, ya ce wannan aiki bai tsaya a kan gina gida kawai ba, domin an haɗa shi da koyon sana’o’i, tallafin nomar gida da samar da filayen kiwon abinci domin tabbatar da samun abinci da ɗan samun kuɗi. A cewarsa, zawarawan da suka nemi tallafi daga gwamnati ne suka fara ɗora tubalin haɗin kai da ya haifar da wannan cigaba.
Daraktan FHFL, Abdulmuttalib Mukhtar, ya ce shirin ya nuna cewa lokacin da al’umma suka ɗauki mataki, gwamnati ta goya musu baya, sauyi na gaskiya kan samu. Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya ƙara da cewa hakan na cikin manufar gwamnati na ganin kuɗin gwamnati ya koma cikin abin da jama’a za su iya gani da amfana da su kai tsaye.
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana aikin a matsayin misalin ingantaccen tsarin mulki mai kallon al’umma da burinsu. Aikin ya ƙirƙiri fiye da ayyuka 500, ya kuma samar da matsuguni mai dorewa ga iyalai 100. A baya-bayan nan, ma’aikatar gidaje ta ƙayyade farashin sabbin gidaje a shirin Renewed Hope Estate domin tabbatar da adalci da sauƙin mallaka ga jama’a a duk faɗin ƙasar.
