Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Lagos ta gano wayoyi 75 da kwamfutoci 5 da wasu barayi suka ajiye yayin da suke gudu a lokacin sintirin jami’an Rapid Response Squad (RRS) a Ikeja. Kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ya bayyana a ranar Asabar 18 ga Oktoba, cewa an gano kayan ne bayan jami’ai sun hango wasu mutum biyu dauke da manyan jakunkuna na “Ghana Must Go” a kusa da Allen Roundabout, inda suka tsere da ganin jami’an tsaro.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa jakunkunan sun ƙunshi iPhones guda 32, wayoyi 38 na kamfanoni daban-daban kamar Samsung, Redmi, Tecno da Honour, kwamfutoci biyar, agogon zamani, AirPods, Samsung Tab da Sorapad. Kwamandan RRS, CSP Shola Jejeloye, ya ce kayan satar ne da barayin suka ajiye da gaggawa yayin da suka tsere. Rundunar ta bukaci duk wanda ya rasa irin wadannan na’urori ya je hedkwatar RRS da shaidar mallaka don karɓar kayansa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Moshood Jimoh, ya yabawa jami’an RRS bisa kwazon da suka nuna, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da dabarun leken asiri da sintiri domin hana laifuka. Ya ce ana ƙara tsaurara tsaro a dukkan sassan jihar don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A wani samame dabam, rundunar ta kama ‘yan wata kungiyar fashi da sace motoci guda hudu, waɗanda ake zargi da kai hare-hare masu hatsari ga direbobi a jihar da maƙwabta. SP Adebisi ya ce an kama su ne tsakanin 15 zuwa 17 ga Oktoba sakamakon binciken sirri da jami’an sashen Tactical Squad suka gudanar. Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
