Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya karyata rahotannin da ke cewa wasu shugabannin jam’iyyar PDP suna matsa masa lamba ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a 2027. A wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulɗar jama’a da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Asabar 18 ga Oktoba, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, ya kuma ce an ƙirƙiri labarin ne kawai don jawo cece-kuce da tada jijiyar wuya a harkokin siyasa.

Olayinka ya bayyana cewa babu wani ɓoyayyen shiri da ake yi domin tilasta wa Wike tsayawa takarar shugabanci, yana mai jaddada cewa matsayinsa a fili yake — goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne har zuwa shekarar 2031. Ya ce Wike mutum ne da yake bayyana matsayinsa a fili, ba ya yin abu a boye.

Dangane da rahoton wani taron PDP da ake zargin an shirya don bawa Wike takara, Olayinka ya fayyace cewa taron da aka yi kawai shi ne na shugabannin PDP daga Kudu a ranar 20 ga Agusta, 2025, wanda ya shafi tsarin rabon mukaman jam’iyya a yankin Kudu. Ya lissafo sunayen shugabanni da ‘yan majalisa daga kudu maso gabas da kudu maso kudu da suka sanya hannu kan sanarwar bayan taron, wadda aka wallafa a manyan jaridu da kafafen watsa labarai na ƙasa.

A ƙarshe, Olayinka ya jaddada cewa Wike ya na nan daram a kan goyon bayan manufofin Shugaba Tinubu da shirin sake tsayawa takara a 2031. Ya ce Ministan zai ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen “Renewed Hope Agenda” a FCT don tabbatar da cewa Abuja ta kai matsayin manyan biranen duniya ta fuskar ci gaba da kayayyakin more rayuwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version