Mataimakin Shugaban Sashen Mai da Iskar Gas na Kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya bayyana cewa sau 22 aka yi ƙoƙarin lalata masana’antar man Dangote, wanda hakan ya sa kamfanin ya gudanar da sauye-sauyen cikin gida da suka haifar da sallamar ma’aikata da dama. Ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a Lagos, inda ya ƙaryata rade-radin cewa matakin ya samo asali ne daga matsin lambar ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN. Edwin ya ce dukkan yunkurin haifqr da tarnaƙi an rubuta su tare da bayanan lokaci da sassan da aka yi ƙoƙarin haddasa gobara, amma tsarin tsaron masana’antar ya hana barnar kai ruwa rana.
Edwin ya jaddada cewa manufar sauye-sauyen ita ce kare amincin da dorewar masana’antar, ba wai amsa wa matsin lambar ƙungiyoyin kwadago ba. Ya bayyana cewa kasancewar masana’antar ta zamani ce mai tsauraran matakan tsaro, duk wani yunkurin tayar da gobara ana dakatar da shi nan take. Wannan na zuwa ne bayan koke-koken ƙungiyoyin kwadago game da sallamar ma’aikata sama da 800 a kamfanin.
A nasa bangaren, Sarkin Ibedaowei na Ekpetiama kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Bayelsa, Bubaraye Dakolo, ya bayyana goyon bayansa ga masana’antar Dangote, yana cewa ta kawo sauyi mai muhimmanci ga harkar mai a Najeriya. Ya ce ganin ana tace man Najeriya a cikin ƙasa ya nuna ana gyara kura-kuran shekaru da dama na dogaro da shigo da mai daga waje. Ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su haɗa kai don tabbatar da cikakken ‘yancin Najeriya wajen samar da man fetur.
Dakolo ya kuma zargi ƙungiyoyin ma’aikata da kasancewa cikin “kabal” da ke hana ci gaba a fannin mai. Ya tunatar da yadda PENGASSAN ta yi yajin aiki a 2007 bayan sayar da kaso 51% na matatun Port Harcourt da Kaduna ga kamfanin Bluestar Oil na Aliko Dangote, wanda hakan ya sa gwamnatin Yar’Adua ta soke yarjejeniyar — lamarin da ya haifar da shekaru 18 na durkushewar matatun Najeriya da asarar biliyoyin daloli. Ya yi kira da kada a sake maimaita irin wannan kuskure, yana mai cewa masana’antar Dangote ba ta da wata takura ga kasuwa, domin gwamnati ta riga ta bayar da lasisin gina matatun mai guda 30, amma wasu masu ruwa da tsaki sun fi son riba ta gaggawa daga shigo da mai fiye da saka hannun jari na dogon lokaci.
