Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta sanar da cafke mutum takwas da ake zargi da kai hare-haren fashi da kisa a sassan jihar, tare da kwato motoci biyu kirar Lexus da wasu kayayyakin da aka sace. Kwamishinan ‘yan sanda Adekimi Ojo ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Ilorin, inda ya ce an samu gagarumar nasara, musamman bayan kama Olatunji Samson, mai shekaru 52, wanda ake zargi da jagorantar fashi a Mai Gida Estate, Amoyo, ranar 21 ga Nuwamba.

Kwamishinan ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 9 na dare, inda barayin suka yi wa mai gidan da mai gadinsa duka, suka daure su, sannan suka gudu da motarsa Lexus RS 350, dala $10,000, naira miliyan 2.95, wayoyi, kayan ado da tufafi. Daga bisani bincike ya kai jami’an zuwa Ibadan, inda barayin suka yi yunkurin sayar da motar da suka sace. Samson, wanda aka kama, ya amsa laifinsa tare da bayyana wasu sace-sacen da suka gabata.

Bechi Hausa ta gano cewa rundunar ta kuma samu nasarar kama wasu da ake zargi da kashe wata ma’aikaciyar otal mai suna Opeyemi Bello a ranar 16 ga Nuwamba, inda Yusuf Ibrahim, tsohon ma’aikacin otal, ya amsa cewa ya shaketa da bargon gado bayan ta hange shi yana kokarin sata. Haka kuma an cafke wasu mutum biyu da aka bi sawu, bayan sace wata wayar iPhone 14 Pro Max da motar Toyota Camry a Basin, Ilorin.

A Offa kuwa, an cafke mutum hudu — Umar Adamu, Aliyu Umar, Lukman Idris da Kazeem Ahmed — bisa zargin kai hare-haren fashi ga ɗalibai, inda aka gano wayoyi da na’urorin lantarki. CP Ojo ya gode wa ‘yan jarida, yana mai cewa za a ci gaba da sintiri da kai farmaki kan miyagu har sai an kawar da dukkanin baragurbi a Kwara.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version