Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sokoto ta sanar da cafke wasu mutane da ake zargi da ɗaukar nauyin ’yan bindiga da kuma satar babura, a jerin samamen da aka gudanar a Sokoto da Zamfara. Kakakin rundunar, Ahmed Rufai, ya ce an kama mutum uku a Tangaza bisa zargin taimaka wa wasu gungun ’yan bindiga wajen sayar da shanun da aka sace.

Rufai ya bayyana cewa ɗaya daga cikin wadanda aka kama, Ruwa Ginyo, wanda shi ne shugaban Fulani na Gidan-Madi, an kama shi da abokan aikinsa biyu tare da gano shanu huɗu da aka sace. Kwamishinan ’yan sanda Ahmed Musa ya bayyana cewa katse hanyoyin kuɗinsu babban nasara ce ga rundunar.

A wani samame da ya biyo baya, rundunar Strike Force ta kutsa Talata Mafara a Jihar Zamfara, inda ta kama wasu da ake zargi da satar babura da sayar da su ta bayan fage. An gano babura biyu da aka sace a Sokoto. Musa ya ce wannan ya nuna yadda rundunar ke fadada ikon aikinta har zuwa jihohi makwabta domin samun nasarar yakar laifi.

Kwamishinan ya gargadi al’umma, musamman masu saye da sayar da dabbobi da babura, da su rika tantance takardun mallaka kafin hulɗa. Ya kuma shawarci jama’a su rika kai rahoton duk wani abin da suka zarga.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version