Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta tabbatar da karɓa tare da sakin ’yan sa-kai shida da sojojin Najeriya suka kama a Jihar Edo a farkon watan Disambar 2025 yayin da suke tafiya a kan hanyar Auchi–Ikpeshi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta fitar, ta ce an miƙa mutanen ga rundunar ’yan sandan Kwara a ranar 31 ga Disamba, bayan bincike da tantancewa daga rundunar soji ta 22 Armoured Brigade da ke Ilorin.
’Yan sandan sun ce bincike ya tabbatar da cewa mutanen ’yan sa-kai ne da ke aiki tare da hukumomin tsaro wajen yaƙi da ’yan fashi da sauran laifuka, inda aka wanke su daga duk wani zargi tare da sakin su ga shugabanninsu, yayin da rundunar ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da bin doka.
