Fitaccen malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya maida martani mai zafi ga masu kira da a kama shi saboda tsokacinsa kan batun tsaro da tattaunawa da ’yan bindiga. Gumi ya zargi masu suka da rashin kishin kasa da jahilci, yana mai cewa ayyukansa na shiga tsakani domin kawo zaman lafiya ba laifi ba ne, kuma bai sabawa doka ko tsarin kasa.

Malamin ya bayyana cewa a 2021 ya je dajin Sabon Garin Yadi a Giwa, Kaduna, tare da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar a lokacin, domin samun sulhu da kusan ’yan bindiga 600 da suka halarci taron. Ya ce su kansu ’yan bindigar sun amince su ajje makamai idan gwamnati ta samar musu da tsaro, guraben raya al’umma da kuma dakatar da kama su ba tare da dalili ba.

Gumi ya ce duk yarjejeniyar da aka cimma ba a cika ta ba, lamarin da ya sa shirin sulhun ya mutu kafin ya tsiro. Ya bayyana takaicinsa cewa maimakon a tambayi gwamnati me ta gaza, wasu ’yan Najeriya sun fi sha’awar neman a kama shi, duk da cewa aikin da ya dauka ya kasance da cikakkiyar sanin hukumomi.

Malamin ya kare kansa, yana cewa tattaunawa da masu laifi ba laifi ba ne idan manufar shi ne hana kashe-kashe da kawo zaman lafiya. Ya kuma yi gargadin cewa rashin jure ra’ayi daban yana kara rikita kasa, tare da addu’ar Allah ya kare Najeriya daga kiyayya da ruɗin siyasa da ke hana a nemo mafita ta gaskiya ga matsalar tsaro.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version