Fitaccen lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa rikicin da ya faru tsakanin Ministan FCT, Nyesom Wike, da wani jami’in Rundunar Ruwa, Lt. Yerima, ya nuna cewa Najeriya har yanzu tana tafiya ne a yanayin mulkin soja. Ya ce doka ta bai wa minista ikon shiga duk wani fili da ke ƙarƙashin gwamnatin Abuja, sannan hana shi shiga da jami’in soja ya yi, ya saba wa dokar Land Use Act.

Falana ya ce tsohon hafsan rundunar ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo, bai da hurumin tura jami’in soja ya tsare masa fili, domin doka ta haramta amfani da sojoji a rigingimun farar hula. Ya kara da cewa Lt. Yerima bai kamata ya karɓi irin wannan umarni ba, domin umarnin da soji zai bi dole ne ya zama na halal kuma ya shafi aikinsa na soja.

Ya soki yadda Minista Wike ya zagi jami’in sojan, yana mai cewa hakan ya keta haƙƙinsa na mutunci. Falana ya ce ministan ya yi sakaci, domin ya kamata ya koma ya kai ƙara ko ya sanar da hukumomin soja maimakon yin faɗa da jami’in. Falana ya kuma bayyana cewa martanin wasu manyan hafsoshin soja da suka goyi bayan Lt. Yerima na nuna yadda Najeriya ta kasa cire salon mulkin soja a cikin gwamnati.

Falana ya ce gwamnati na da alhakin magance irin wannan rikici ta bin doka, musamman ganin yadda jama’a suka nuna goyon baya ga jami’in soja saboda halayen Wike da ake kallon sun yi tsauri. Ya yi kira da gwamnati ta tabbatar da bin doka a rigingimun ƙasa da harkokin gine-gine, tare da nisantar da jami’an tsaro daga shiga rigingimun farar hula domin kiyaye martabar dimokuraɗiyya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version