Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang, ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyarsa ta PDP ta ɗauka na korar Ministan Abuja, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. A cewar Muftwang, wannan mataki ba a tattauna shi a tsakanin majalisar gwamnonin PDP ko kwamitin zartarwa ba kafin a gabatar da shi a gaban babban taron jam’iyyar na ƙasa.
A ranar Asabar ce PDP ta sanar da korar Wike tare da sakataren jam’iyya na ƙasa, Samuel Anyanwu, da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, bisa zargin su da zagon ƙasa ga jam’iyyar. Wannan hukunci ya ƙara zafafa cece-kuce a cikin jam’iyyar da ke fama da rikice-rikicen cikin gida.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Muftwang ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa korar manyan jiga-jigan jam’iyyar a lokaci irin wannan ba dabara ba ce, kuma ba zai taimaka wajen warware rikice-rikicen da suka addabi PDP ba. Ya ce akwai bukatar a nemi hanyoyin sasanci maimakon ɗaukar matakan da za su kara rikitar da jam’iyyar.
Wannan matsayi na Muftwang ya fito ne bayan Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, shi ma ya bayyana rashin goyon bayansa ga dakatar da Wike da abokan siyasarsa. Masu lura da al’amura na ganin cewa wannan sabbin abubuwan na iya kara lalata daidaituwar PDP a matakin kasa.
