Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari garin Tsamiya da ke Karamar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi ranar Asabar, inda suka kona wurin binciken jami’an Hukumar NSCDC. Harin ya kuma shafi wani gidan karuwai da gidan wani mutum mai suna Sule Mai Goge.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da Alhaji Yusuf Bazamfare yayin harin da suka kai wa al’ummar yankin.

Rundunar ’yan sandan ta ce ta tura jami’an tsaro na musamman zuwa garin Tsamiya domin daƙile matsalar. Ta kuma bayyana cewa an fara bincike kan lamarin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto wanda aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version