Iyayen Maimuna Sani (Nihal), daliba mai shekaru 14 a makarantar sakandiren St.Louis da ke Kano, sun bukaci a gudanar da cikakken bincike kan rasuwarta bayan rahotanni masu karo da juna kan musabbabin mutuwarta a makarantar kwana.

Mahaifiyarta, Nusaiba, ta ce an sanar da ita cewa ‘yarta ba ta da lafiya kuma tana asibiti, amma daga baya aka tabbatar mata da mutuwarta. Iyalan sun nuna shakku kan bayanin makarantar cewa Nihal ta mutu ne sakamakon cutar asma, yayin da wasu bayanai ke cewa an hukunta ta ne kafin lamarin ya faru.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kafa kwamitin bincike na musamman domin gano hakikanin abin da ya jawo rasuwar dalibar. Gwamnatin jihar ta ce za ta dauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken, yayin da iyalan marigayiyar ke ci gaba da neman a tabbatar da adalci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version