Tsofaffin hafsoshin sojin Najeriya da abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (rtd) sun bukaci a yi wa tsarin tsaron ƙasar garambawul bayan rasuwarsa a hannun wasu ƴan bindiga da suka sace shi a jihar Katsina.
An bayyana wannan kira ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Alhamis, inda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (rtd) ya yi magana a madadin abokan aiki da makusantan marigayin. A taron, an jaddada buƙatar ɗaukar matakan da za su ƙarfafa yaƙi da matsalar rashin tsaro.
Da yake magana kan ƙwarewarsa bayan ya shafe lokaci a hannun ƴan bindiga, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (rtd) ya ce akwai buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai domin wargaza ayyukan masu tayar da ƙayar baya. Ya kuma bayyana cewa ƙungiyoyin ƴan ta’adda da ƴan bindiga ba sa miƙa wuya cikin sauƙi ta hanyar tattaunawa kawai, yana mai cewa dole ne a fuskance su da matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya.
