Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wasu manyan ‘yan fashi da makami guda tara tare da kwato mugayen makamai da mota, a wani gagarumin samame da ta kai a Kano da Kaduna. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, a ranar Litinin, 13 ga Oktoba, 2025. Ya ce an kama su ne bayan fashin da aka yi a unguwar Dorayi Babba ranar 8 ga Oktoba, inda ‘yan fashin suka kwace mota kirar Toyota Yaris, kudi kusan Naira miliyan 3.7, wayoyi da wasu kayayyaki, tare da jikkata matar gidan da suka kai wa harin.

Bisa umarnin IGP Kayode Egbetokun, jami’an rundunar suka yi gaggawar kai samame inda suka kama mutum daya nan take, sannan rundunar Special Intervention Squad ta cafke sauran takwas daga bisani. Wadanda aka kama suna da shekaru tsakanin 17 zuwa 24, kuma sun amsa laifukansu tare da bayyana yadda suka aikata fashi a Kano, Kaduna da Abuja. An kwato daga hannunsu bindigogi guda uku, harsasai 18, wukake, adduna, fitilu, abin yankan ƙarfe da mota kirar Toyota Corolla LE da suke amfani da ita wajen fashi.

Kwamishinan ya bayyana cewa za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike. Ya yaba wa jami’an rundunar bisa jajircewa da nasarar da suka samu, tare da godewa al’umma bisa bayar da bayanai. Haka kuma ya jaddada cewa shirin “Operation Kukan Kura” ya taimaka matuka wajen rage fashi, sata da tada zaune tsaye a Kano, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da hadin kai domin tabbatar da tsaro.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version