Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita cikin Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Tahir ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir tare da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, a lokacin da ya shigo ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Ya ce jami’an hukumar sun gano motar ne yayin binciken ababen hawa da ke shiga ƙasar.
Hukumar ta bayyana cewa an fara shirye-shiryen miƙa wanda ake zargin ga rundunar ‘yan sandan jihar domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Tahir ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron iyakoki, da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya.
