Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta tabbatar da Honarabul Nasiru Sule Garo a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaɓen 2027. Hakan ya biyo bayan sauya Engineer Sunusi Danbatta da jam’iyyar ta yi da Garo.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Usaini Isa Mai Riga, ya ce an yanke shawarar ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma duba ƙwarewar Garo, wanda ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya. Ya ce wannan ya kammala tsarin cikin gida na zaɓen ɗan takarar.

Danbatta ya ce janyewarsa daga takarar da son ransa ne, yana mai cewa zai ci gaba da goyon bayan Garo da sauran ’yan takarar jam’iyyar domin ganin NDC ta yi nasara a 2027. Shi ma Garo ya yi alƙawarin tafiya da dukkan mambobin jam’iyyar tare da samar da wakilci mai inganci idan aka zaɓe shi.

Sakataren shirya ayyukan jam’iyyar na jihar, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya ce fitowar Garo za ta ƙarfafa shirye-shiryen NDC a Kano ta Arewa. Ya ce kamfen ɗin jam’iyyar zai fi mayar da hankali kan ƙarfafa tattalin arziki, noma, ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da ingantaccen wakilci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version