Fiye da mutane 500 sun kai takardunsu Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsaren Gine-gine ta Jihar Kano domin tantance ikirarin mallakar filayen da ake takaddama a kansu a Rimin Zakara, Ƙaramar Hukumar Ungogo, amma kusan 80 ne kawai suka kai matakin tantancewa na biyu a DSS.

Kwamishinan ma’aikatar, Abduljabbar Muhammad Umar Garko, ya bayyana hakan yayin ganawa da ’yan jarida a Kano ranar Asabar. Ya ce gwamnati ta raba aikin tantancewar zuwa matakai biyu domin hana zamba da sauran matsalolin da suka shafi mu’amalar filaye a yankin.

Ya ce a matakin farko, masu neman diyya suna kai takardun mallakarsu ma’aikatar domin tantance su, sannan su wuce DSS domin ƙarin bincike. Matakin na biyu ya haɗa da tantance bayanan mutum ta hanyar na’urar zamani da ɗaukar yatsun hannu kafin a yi la’akari da biyan diyya.

Kwamishinan ya ce tsarin na da nufin tabbatar da cewa diyya ta isa ga haƙiƙanin masu filayen da aka tabbatar da mallakarsu. Ya ƙara da cewa gwamnati na son hana ikirarin bogi, ikirarin fili fiye da sau ɗaya da sauran abubuwan da za su iya jawo biyan kuɗin gwamnati ga waɗanda ba su cancanta ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version