Hon. Abdullahi Zubairu Abiya ya bayyana a matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, biyo bayan tsige tsohon shugaban jam’iyyar na jiha, Hashimu Dungurawa. An amince da nadin nasa ne bayan taron gaggawa da Kwamitin Zartarwa na jiha (State EXCO) ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar.

Mataimakin Mashawarcin Shari’a na jam’iyyar, Barrista Yusuf Mukhtar, ne ya sanar da matakin, inda ya ce an dauki shi ne bisa tanadin kundin tsarin NNPP. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya biyo bayan mika kudurin tsige Dungurawa da Kwamitin Zartarwa na Karamar Hukumar Dawakin Tofa ya gabatar wa shugabancin jiha.

Tun da farko, EXCO na Dawakin Tofa karkashin Hon. Abdullahi Ali Uban Iya Dawanau ya mika kudurin da EXCO na Unguwar Gargari ya dauka, inda aka zargi Dungurawa da aikata ayyukan da suka saba wa jam’iyya. Bayan duba rahoton, State EXCO ya amince da tsige shi tare da tabbatar da Abiya a matsayin mukaddashin shugaba.

A martaninsa, Hon. Abdullahi Zubairu Imam Abiya ya ce jam’iyyar za ta yi adalci ga kowa, tare da ci gaba da kasancewa mai biyayya ga jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version