Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar haɗaka ta African Democratic Congress (ADC). Obi ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Enugu, babban birnin Jihar Enugu, tare da magoya bayansa da shugabannin siyasa.
A yayin jawabin nasa, Obi ya ce bayan watanni na tuntuɓa da tattaunawa, shi da sauran shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun yanke shawarar shiga ADC domin haɗa ƙarfi da sauran jam’iyyun adawa a faɗin ƙasar. Ya bayyana cewa matakin na da nufin gina haɗaka mai ƙarfi a fagen siyasar Nijeriya.
Obi ya ce burinsu shi ne ceto Nijeriya daga mummunar shugabanci, tare da yin duk mai yiwuwa domin daƙile maguɗi da murɗiyar zaɓe a babban zaɓen 2027. Ya ƙara da cewa taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da tsofaffin gwamnoni da shugabannin siyasar Kudu maso Gabas.
