Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Talata a kan titin Dutse–Kiyawa, a yankin Dan Masara Quarters da ke Dutse, Jihar Jigawa. Lamarin ya shafi haɗuwar motoci da dama a lokaci guda.

Shugaban FRSC, Malam Shehu Mohammed, ya ce binciken farko ya nuna gudu fiye da kima da fashewar taya ne suka haddasa hatsarin, wanda ya sa direbobi suka rasa iko da motoci. Hatsarin ya shafi motocin haya kirar Volkswagen Golf guda biyu da kuma babbar motar dakon kaya kirar Mercedes-Benz.

Ya bayyana cewa mutane 20 ne ke cikin motocin, inda 18 suka mutu, yayin da mutum biyu suka jikkata da raunuka daban-daban. FRSC ta ce tawagar ceto ta isa wurin cikin ƙasa da minti biyar bayan kiran gaggawa, tare da kwashe waɗanda abin ya shafa zuwa Asibitin Dutse, tana mai kira ga direbobi da su kiyaye gudu da kula da lafiyar motocinsu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version