Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kama wani mutum da ake zargin ɗan kunar baƙin wake ne a Jihar Borno, a yayin wani samame da dakarun Operation Hadin Kai suka gudanar. Rundunar ta bayyana hakan ne ta shafinta na X, inda ta ce an kuma ƙwace kayayyakin haɗa bam daga hannunsa.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bama ne, kuma an same shi da wasu kayayyaki masu alaƙa da ayyukan ta’addanci. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce an kama mutumin da bama-baman da aka riga aka haɗa, abin da ke nuna shirin kai hari.
Rundunar ta ce a halin yanzu wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike. An ce ana zurfafa binciken ne don gano masu ɗaukar nauyinsa, abokan aikinsa da kuma alaƙarsa da ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a yankin.
