Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce har yanzu wasu daga cikin abubuwan da suka jawo yaƙin basasar Najeriya na shekarar 1967 suna nan, yana mai jaddada cewa dole ne a yi duk mai yiwuwa domin hana sake aukuwar irin wannan rikici. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin karɓar bayanai da aka tattara kan kisan gillar Asaba a ɗakin karatunsa da ke Abeokuta.
Obasanjo ya ce Najeriya ta fuskanci yaƙin basasa sau ɗaya, kuma hakan ya isa, yana mai cewa Allah Ya kiyaye ƙasar daga sake fuskantar irin wannan bala’i. Ya buƙaci ‘yan Najeriya su fahimci darussan tarihi, su yi Allah-wadai da abubuwan da ba su dace ba, tare da ɗaukar alƙawarin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.
Ya kuma yaba wa Chief Chuck Nduka-Eze kan ƙoƙarinsa na tattara tarihin kisan gillar Asaba, yana mai cewa adana tarihi na taimakawa wajen warkar da raunukan ƙasa da ƙarfafa haɗin kai. Obasanjo ya ce zai yi duk abin da zai iya domin tabbatar da cewa Najeriya ba ta sake shiga yaƙin basasa ba.

