Hukumar Hisbah ta Malumfashi a Jihar Katsina ta sanar da sabbin ƙa’idoji shida da ta buƙaci masu sana’ar Adaidaita Sahu su bi yayin gudanar da ayyukansu. Ta ce matakin na da nufin inganta ɗabi’a da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.
Daga cikin ƙa’idojin akwai hana ɗaukar mata a gaban Adaidaita Sahu, sanya gajeren wando ko singileti yayin aiki, kunna kiɗan da ke takura wa jama’a, ɗaukar kayan da ake zargi da alaƙa da laifi, da kuma rufe labulen Adaidaita Sahu ba tare da dalilin ruwan sama ko tsananin sanyi ba.
Hukumar ta kuma haramta tukin ganganci musamman a lokutan bukukuwa, tare da gargaɗin cewa duk wanda aka samu ya karya waɗannan ƙa’idoji zai fuskanci hukunci. Sanarwar ta fito ne daga sashen fasahar sadarwa na Hukumar Hisbah ta Malumfashi.

