Jam’iyyar haɗakar ’yan adawa ta African Democratic Congress (ADC) ta nuna damuwa kan ƙalubalen da ’yan Najeriya ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji nan take.

ADC ta ce aiwatar da dokar zai ƙara tsananta matsin rayuwa ga talakawa, musamman ma a halin da ƙasar ke ciki na tsadar rayuwa da matsalolin tattalin arziki.

A cikin sanarwa, jam’iyyar ta jaddada buƙatar tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago, fararen hula, ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa, ƙwararru da gwamnatocin jihohi kafin ɗaukar mataki, tare da samar da matakan kariya don kare talakawa daga ƙarin nauyi.

ADC ta kuma ce gwamnati ya kamata ta mayar da hankali kan harajin kayan alatu, ribar da ta wuce kima daga manyan kamfanoni, da yaƙi da cin hanci da rashawa, maimakon ɗora haraji kan talakawan da ke fama da tsadar rayuwa, tare da yin gargaɗin cewa tilasta dokar ba tare da tattaunawa ba zai jawo sakamako mara kyau ga tattalin arziki da zamantakewa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version