Sauyin shugabannin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na iya haifar da babban canji a rundunonin sojin Najeriya, inda akalla janar 60 ake sa ran za su yi ritaya daga aiki. Wannan sauyi ya biyo bayan cire Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Shugaban Rundunar Tsaro (CDS), tare da wasu manyan hafsoshi.
A sabon tsarin, tsohon Shugaban Sojojin Ƙasa, Lieutenant Janar Olufemi Oluyede, ya zama sabon CDS, yayin da Manjo Janar Waidi Shaibu ya zama Shugaban Sojojin Ƙasa, Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke ya karɓi mukamin Shugaban Sojojin Sama, kuma Rear Admiral Idi Abbas ya zama Shugaban Sojojin Ruwa. Manjo Janar E.A.P. Undiendeye kuwa ya ci gaba da rike mukaminsa na Shugaban Leken Asiri na Tsaro.
Majiyoyi daga rundunar soji sun tabbatar da cewa wannan sauyi zai tilasta wa manyan hafsoshi da suka fi sabbin shugabannin shekaru su bar aiki, domin kiyaye tsarin da’a da girmamawa a rundunar. Wadanda abin zai shafa sun haɗa da jami’an da suka fito daga NDA Regular Courses 38, 39, da kuma wasu daga Course 40.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa wannan sauyi ba wai saboda jita-jitar juyin mulki ba ne, sai dai wani yunkuri ne na ƙarfafa tsaro da inganta haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro. Wasu masana tsaro sun ce sauyin zai buɗe sabuwar dama ga ƙarni na gaba na hafsoshi masu sabbin tunani, yayin da tsohon kakakin rundunar soji, Brig. Janar Sani Usman Kukasheka (rtd), ya bayyana matakin a matsayin “na yau da kullum” a tsarin soja domin kawo sabon kuzari a ayyuka.
