Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gudanar da babban sauyi a manyan mukaman tsaro na ƙasar, inda ya sauke Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, tare da wasu shugabannin rundunonin soja. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yada labarai, Sunday Dare, ya fitar a ranar Juma’a. A cewar sanarwar, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Tarayya na sake gina tsarin tsaro da ƙarfafa ingancin rundunonin sojoji.
A cikin sabbin nade-naden, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa domin maye gurbin Janar Musa. Haka kuma, Major-General W. Shaibu ya zama sabon Babban Hafsan Soja, Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama Babban Hafsan Sojin Sama, yayin da Rear Admiral I. Abbas ya karɓi ragamar Babban Hafsan Rundunar Ruwa. Sai dai Major-General E.A.P. Undiendeye ya ci gaba da zama Babban Daraktan Leken Asirin Tsaro.
Shugaba Tinubu ya gode wa hafsoshin da aka sauke bisa jajircewar da suka nuna wajen kare ƙasar, tare da kira ga sabbin shugabannin da su tabbatar sun ba da cikakken gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ƙwarewa da haɗin kai a tsakanin rundunonin tsaro domin amfanin ƙasa baki ɗaya.
