Sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa zai kare dokokin zaɓe da na kundin tsarin mulkin Najeriya, tare da tabbatar da gudanar da zaɓe mai sahihanci da gaskiya a duk faɗin ƙasar.
Amupitan ya yi wannan bayani ne bayan rantsar da shi a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da ya tabbatar da cewa dukkan zabubbuka masu zuwa za su kasance cikin gaskiya, tsabta da inganci.
A cewar sabon shugaban, nasarar gudanar da zaɓe mai kyau ba za ta samu ba sai da haddin kai daga masu ruwa da tsaki, ciki har da jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula, da hukumomin tsaro. Ya ce zai yi aiki kafada da kafada da su domin tabbatar da an samu ci gaba a tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Farfesa Amupitan shi ne shugaban INEC na shida tun bayan da Najeriya ta koma tafarkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, kuma ya jaddada cewa zai yi aiki da tsoron Allah wajen kare amana da tabbatar da sahihin tsarin zaɓe da zai ƙara wa jama’a amincewa da hukumar.
