Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta gargaɗi gwamnatin tarayya cewa za ta ɗauki mataki idan ba a kammala biyan albashin malamai da duk wasu alawus-alawus kamar yadda aka amince a yarjejeniyar 2025 ba kafin ƙarshen watan Maris.
Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya bayyana cewa duk da an samu ɗan sauyi tun daga watan Janairu, har yanzu ba a kammala aiwatar da tsarin ba, musamman ga wasu malamai da ke kan aiki na wucin gadi ko ziyara. Ya ce wasu muhimman hakkoki kamar alawus ɗin EAA har yanzu ba a biya su gaba ɗaya ba.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan jinkirin kasafin kuɗi da kuma yadda gwamnati ke karkata hankali zuwa harkokin siyasa, tana mai cewa idan ba a cika yarjejeniyar ba zuwa ƙarshen watan, za su ɗauki matakin da ya dace bisa ƙa’ida.


